Shugaban majalisar dokokin kasar Iran kuma shugaban tawagar tattaunawa da kasar Amurka ya bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan yan siyasa masu goyon bayan Trump da Jam’iyarsa sun yi rauni, ko kuma sun kammala ayyukansu, don haka haramtacciyar kasar Isra’il (HKI) ta bawa kafafen yada labaran Amurka aiki na kirkiro labaran karya kan JMI, da nufin samun goyon bayan Amurkawa na sake komawa yaki da Iran.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, a halin yanzu tashar talabijan ta CNN da kuma jaridu kamar NewYork Times duk sun sami wani sabon aiki na yada karya dangane da Jumhuriyar Musulunci ta Iran (JMI).
Abin lura anan shi ne, Larry Ellison shine babban kula da kudade na sirri na rundunar sojojin Isra’ila, kuma fitaccen mutum a cikin iyalan Ellison a matsayin sabbin mamallakan tashar talabijan ta CNN. A Amurka.
Don haka acikin yan kwanakin dasuka gabata, sun fara yada karyakin kan JMI don cimma manufar HKI na sake komawa yaki da JMI, kuma tana son a wannan karon ma Amurka ta kasance tare da su. Duk farfa gandar su ta soma wani yaki karya ce.