Qalibaf: Isra’ila Tana Son Yakin Amurka Da Iran Ya Ci Gaba

Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya suna ƙoƙarin jawo Amurka zuwa yaƙi marar iyaka da Iran Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir

Kakakin Majalisar Dokokin Iran ya bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya suna ƙoƙarin jawo Amurka zuwa yaƙi marar iyaka da Iran

Kakakin Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan Sahayoniyya suna ƙoƙarin jawo Amurka cikin yaƙi marar iyaka da Iran, yana mai ƙarawa da cewa: Babu wani shugaban Amurka ko na yanzu ko na gaba, a jam’iyyun Republican ko Democrat da zai iya tserewa daga wannan rudanin.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, Qalibaf ya rubuta a dandalin X cewa: Yahudawan Sahayoniyya suna aiki dare da rana don jawo Amurka cikin yaƙi marar iyaka da Iran.”

Ya ƙara da cewa: “Babu wani shugaban Amurka, ko na yanzu ko na gaba, daga Republican ko Democrat, da zai iya tserewa daga wannan rudanin.”

Ya kammala da cewa: “Muddin Amurka ba ta yi watsi da tunanin ‘Isra’ila ta Farko’ ba, Amurka da kawayenta suna kan hanyarsu ta zuwa wani zamani mai duhu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted