Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya isa kasar Sin domin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu inda zai gana da takwaransa Xi Jinping.
Wasu hotuna da aka watsa a gidan talabijin na kasar Rasha sun nuna cewa, shugaban fadar Kremlin ya sauka birnin Beijing, inda ya samu tarba daga wasu jami’an kasar Sin.
Wannan shi ne karo na farko da Vladimir Putin ya kai ziyara wata kasar waje tun bayan sake zabensa a watan Maris, kuma karo na biyu da ya je China cikin sama da watanni shida.
A yayin ziyarar tasa, shugaban na Rasha zai ziyarci birane biyu – Beijing da Harbin.
A yayin ziyarar shugabannin kasashen biyu za su tattaunawa kan batutuwa daban-daban.
Za su yi musayar ra’ayi kan batutuwan da suka fi daukar hankalin duniya da na shiyya-shiyya sannan kuma Shugabannin biyu za su halarci bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Rasha da Sin.