Shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiya ya bayyana nasarar kwato garin susangerd a matsayin wata alama ta karfin hadin guiwa da kuma amincewa juna da ake da shi, da kuma sanya muradun kasa a gaba fiye da duk wani banbanci ko ra’ayi na kashin kai ko na siyasa
A cikin wani sako da ya aike da shi game da bikin tunawa da yanton susangard, shugaban iran ya jaddada cewa wanan nasarar da aka samu a cikin mawuyacin lokaci ta sanya susangerd ta zama alama ta karfin hadin guiwa da kuma dunkulewa kan manufa guda, musaman idan aka sanya moriya da walwalarta a gaba fiye da duk ani sabani ko ra’ayoyin mutum daya ko na siyasa
Haka zalika sakon ya kara da cewa wannan gogewar ta tarihi ta nuna cewa idan alumma da dakarun tsaro da kuma jami’an gwamnati suka bi tafarki daya, game da makomar kasar to zaa iya kawar da kowacce irin barazana da tafi kowacce girma da karfi ta hanyar jajircewa da kuma hadin kai