Pezeshkian : Zamu Mayar Da Martani Ga Duk Wata Wauta Ta Kaiwa Kasarmu Hari

Shugaba kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa al’ummar Iran za su mayar da martani cikin hikima kan duk wata wauta na kai wa

Shugaba kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa al’ummar Iran za su mayar da martani cikin hikima kan duk wata wauta na kai wa kasar hari.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan da rundunar sojin saman Iran ta tabbatar da hare-haren da Isra’ila ta kai a yankunan Tehran, Khuzestan, da Ilam, inda ta ce an yi nasarar dakile harin.

Rundunar sojin Iran ta ce jami’anta hudu sun yi shahada a hare-haren, na Isra’ila kan wasu sansanonin soji a fadin kasar ya karu zuwa hudu.

Pezeshkian ya jinjinawa wadanda abin ya shafa saboda sadaukar da rayukansu don kare kasar, tare da jajantawa Sojoji, da al’ummar kasar kan shahadarsu.

A wani labarin kuma ‘yan sandan Iran 10 ne suka yi shahada a wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai a lardin Sistan da Balouchestan da ke kudu maso gabashin kasar a ranar Asabar.

Har zuwa lokacin fasara wadannan labaren babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments