Pezeshkian yayin ganawa da Macron ya soki Faransa kan goyon bayan Isra’ila

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya caccaki Faransa da sauran kasashen yammacin duniya saboda bayyana kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a matsayin “kare kai”

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya caccaki Faransa da sauran kasashen yammacin duniya saboda bayyana kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a matsayin “kare kai” inda ya bayyana  hakan a wata ganawa da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron.

“A kan wace doka za a iya tabbatar da laifukan Sahayoniyawan, wanda Amurka da wasu kasashen yamma kamar Faransa, suka bayyana a matsayin halaltacciyar kariyar kai?” kamar yadda  Pezeshkian ya ce a  gefen taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Ya kara da cewa, “Kasashen yammacin duniya ya kamata su daina yin amfani da salon siyasar harshen damo, domin hakan yana karfafa gwiwar Isra’ila wajen aikata laifukan yaki.

Pezeshkian ya ce duk da cewa masu fafutukar kare hakkin bil’adama sukan bayyana ra’ayinsu tare da sauran jama’ar duniya kan zalunci da Isra’ila ke yi, amma duk da hakan yahudawan  sun ci gaba da yin ta’asar da suke yi a kan dubban mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza da Lebanon.

Ya ce Iran, domin hana tashe-tashen hankula da rikice-rikice a yankin, tana yin taka-tsan-tsan wajen mayar da martani kan kisan da Isra’ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran.

Pezeshkian ya ce “A akasin haka, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana  kara kaimi wajen aikata laifuka a Gaza, kuma a halin yanzu tana kai hari kan kasar Lebanon.”

“Al’ummar Iran da na yankin suna fuskantar mummunar illa daga laifukan gwamnatin sahyoniyawan, kuma ci gaba da wannan ta’asa na iya karkatar da lamarin zuwa wani abu daban da ba a fatar faruwarsa.”

Shugaban na Iran ya ce Faransa za ta iya taka rawar gani wajen kawo karshen laifukan Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments