Pezeshkian: Makiya Sun Gaza Cimma Mummunar Manufarsu

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Makiya sun gaza a shirye-shiryensu duk da yunƙurin da suka yi na kakaba yaƙi da kuma gurgunta ƙasar Shugaban

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Makiya sun gaza a shirye-shiryensu duk da yunƙurin da suka yi na kakaba yaƙi da kuma gurgunta ƙasar

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Duk da yunƙurin maƙiya na daukan matakin yaƙi da kuma ƙoƙarin da suke yi na kawo cikas ga ayyukan ƙasar, amma sun gaza cimma burinsu. Ya yaba da muhimmiyar rawar da jiragen sufuri na ƙasar Iran suka taka a lokacin yaƙin kwanaki 40.

A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Shugaban kasa Pezeshkian, a lokacin ganawarsa da wakilan jiragen sufuri na ƙasa, shugabannin ƙungiyoyin sufuri da fasinjoji da kuma ƙungiyar direbobi waɗanda suka ba da gudummawa ga ƙoƙarin rusa maufar makiya a lokacin yaƙin kwanaki 40, ya jaddada muhimmancin ƙarfafa ikon ƙungiyoyin ma’aikata, gyara hanyoyin samar da kayan aiki da rarrabawa da kuma magance ƙalubalen da suka shafi inshora da haraji da direbobi ke fuskanta. Ya kuma jaddada buƙatar hanzarta warware buƙatunsu kuma ya umurci hukumomin zartarwa da suka dace da su daidaita da kuma sa ido sosai kan waɗannan batutuwa.

Shugaban kasar Iran ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma jaddada haɗin gwiwa a cikin tsarin ci gaba, yana mai bayyana cewa: “Gina ƙasa yana buƙatar haɗin kai da haɗin gwiwa; yayin da gwamnati ke ɗaukar nauyin yi wa mutane hidima, masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki da zamantakewa suna ba da gudummawa wajen tallafawa ‘yan ƙasa ta hanyar samar da ayyuka masu kima da muhimmanci.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted