Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi gargadin cewa duk wani harin da Isra’ila za ta kai wa kasar zai fuskanci martanin da ya dace.
Shugaban ya bayyana hakan ne yau yayin wata ziyara a ofishin kungiyar Hamas da ke birnin Tehran, inda ya karrama Yahya Sinwar shugaban kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, wanda ya yi shahada a yakin da suka yi da sojojin Isra’ila a zirin Gaza a makon jiya.
Tun a farkon watan Oktoban 2023, Isra’ila ta fara kai munanan hare-hare a Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 42,600 da kuma wasu 2,483 a Lebanon.
Pezeshkian Ya kuma jaddada cewa, wannan ba yaki ne da za a iya kawo karshensa ta hanyar kashe mutane ba, amma yaki ne da za a iya kawo karshensa ta hanyar tabbatar da adalci da kuma la’akari da ‘yancin kowa da kowa, wani abu da ba zai yiwu ba ta hanyar karfi da rashin adalci.
A baya-bayan nan dai Isra’ila ta kara kaimi kan barazanar da take yi kan Iran, a daidai lokacin da rahotanni ke bayyana cewa gwamnatin mamayar na iya kai hare-hare kan cibiyoyin soji, ko na man fetur ko makaman nukiliya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.