Palasdinawa Ne Zasu Fayyanace Makomarsu Ba Wasu Dan Mulkin Mallaka Ba: Qalibof

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa falasdinawa masu kasa ne zasu fayyace makomar kasarsu, don haka shirin da wasu manya-manyan kasashen duniya suke dashi a kan makomar Falasdinu da Falasdinawa ba dai-dai bane kuma zamu yi yaki da shi.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Teran ta nakalto shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammada Bakir Qolibft yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokoki na kasashen Asia a birnin Baku na kasar Azaibaijan.

Qolibof ya kuma kara da cewa shirin shugaban kasar Amurka yake yi na kwace gaza da kuma inda za’a maida Falasdinawa ba zai kai ga nasara ba.

Qalibof ya yi allawadai wadai da shugaba Trump kan shishigin da yake yi a cikin al-amuran Falasdinawa, da kuma yin watsi da kokarin Falasdinawa a gaza suke yi don kwato kasarsu.

Ya ce Iran ba za ta amince da duk wata kasa mai jin tana da karfi wacce za ta dorawa falasdinawa tunaninsa ba.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa yakin da HKI ta fafata da falasdinawa a Gaza, da kuma kungiyar Hizbulla a kasar Lebanon, sun bayyana raunin HKI a fili, wannan duk tare da dukkan tallafin da take samu daga kasashen yamma musamman Amurka.

Daga karshe ya ce dole ne a sami yentacciyar kasar Palasdinu mai zaman kanta nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments