Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan.

Rahotanni sun bayyana cewa cewa kasar Pakistan ta bayyana cewa za ta dauki mataken da suka dace wajen kare tsaron alummarta da kasarta bayan kawo

Rahotanni sun bayyana cewa cewa kasar Pakistan ta bayyana cewa za ta dauki mataken da suka dace wajen kare tsaron alummarta da kasarta bayan kawo karshen yajejeniyar dakatar da bude wata ta kwanaki 4 tsakaninsu da kasar Afghanistan  ba tare da wani ci gaba da aka samu ba,

Yarjejeniyar ta waste ne kwana daya kafin cikarta bayan wani mummunan fada da aka tsakanin kasashen biyu da ya jawo dama suka mutu ciki har da fararen hula, Pakistan na zargin Afghanisatan da boye kungiyoyin yan ta’adda dake kai hare-haren ketare iyaka, sai da Kabul ta musanta wannan zargin kuma ta dage akan ikonta,

A karshen mako ne minsitan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya yi barazanar barkewar yaki tsakani, idan dai mataken diplomasiya suka kasa yin amfani,

Ya zuwa yanzu dai jami’in gmwanatin Afghanisyan ba su ce komai game da lamrin ba, sai dai kafafen yada labaran na cikin gida sun nakalto wani wakilin kungiyar Taliban yana siffata bukatun kasar pakistan amatsayin mara muhimmanci kuma ba za’a taba amince da su ba, sai da sun jaddda cewa tattaunawa itace hanyar da tafi dacewa wajen kawo karshen rikicin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments