Majiyar sojojin kasar Pakistan ta bayyana cewa sojojin sun kasha yan ta’adda 12 a wani harin da suka kai kansu a wani shingen da suka kafa a garin Bajaur a yayinda suka rasa sojoji 11 a ranar litinin da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin kasar ta Pakistan sun sha alwashin murkushe yan ta’adda wadanda tace suke samun goyon baya daga kasashen waje. Labarin ya kara da cewa hare-haren ranar 16 ga watan fabrayru a zo ne a dai dai lokacinda gamayyar Jami’an tsaron kasar suke aikin tabbatar da tsaro a garin na Bajaur, wanda ya sami maida martani mai tsanani daga sojoji da kuma sauran jami’an tsaro.
Wannan ya faru ne kafin yan ta’addan su tada bom mai karfi wanda ya lalata ginin da Jami’an tsaron suke amfani da shi da kuma wasu gine-ginen gidajen mutanen gari da suke kusa da shi.
Banda haka wata yarinya guda ta rasa ranta a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Daga ciki har da mata da yara.
Rahoton ISPR na sojojin kasar ta Pakistan ta kamala da cewa yanta’addan wadanda suke samun goyon bayan kasar Indiya ana kiransu ‘Fitna Al-Khawarij’. Kuma kasar Pakistan zata kawar da su kwatakwata daga yankin.