Pakistan: Makaman Nukiliyarmu Suna Cikin Yarjejeniyar Tsaro Da Mu Ka Kulla Da Saudiyya

Ministan tsaron kasar Pakitsan Khaje Asif ya fada a jiya Juma’a cewa, makaman Nukiliyar da kasarsa take da su, wani sashe ne na yarjejeniyar tsaro

Ministan tsaron kasar Pakitsan Khaje Asif ya fada a jiya Juma’a cewa, makaman Nukiliyar da kasarsa take da su, wani sashe ne na yarjejeniyar tsaro da su ka kulla da kasar Saudiyya. Haka nan kuma ya kara da cewa; Yarjejeniyar ta tsaro ce tsagwaronsa, kuma manufarta ita ce aiki tare a tsakanin kasashen biyu a wannan fagen.

Asif wanda tashar talabijin din “Geo News” ta yi hira da shi ya kuma ce; Idan daya daga cikin kasashen ta fuskanci hari,to za mu mayar da martani na hadin gwiwa.”

Ministan tsaron na kasar Pakistan ya kuma ce; Ba tare da ambaton suna ba,amma duk wanda ya kai harin wuce gona da iri, to zai fuskanci mayar da martani na hadin gwiwa.

Da yake amsa tambaya akan ko sun shawarci Amurka akan kulla wannan irin yarjejeniya ta tsaro da Saudiyya, ministan tsaron na kasar Pakistan ya ce, babu bukatar a shigar da wani bangare na uku a cikin batun.

Da yake magana akan sauye-sauyen siyasa da suke faruwa a duniya, ministan tsaron Pakistan Asif ya ce; Ba da jimawa ba, kasar China za ta zama mai jagorantar duniya.

A ranar Laraba din da ta gabata ne dai kasashen Pakistan da Saudiyya su  ka kulla yarjejeniyar tsaro,wacce fira minista Shahbaz da yarima mai jiran gado Muhamad Bin Salman su ka rattaba hannu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted