Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kuma kawayensu na wajen kungiyar sunce zasu kara yawan man fetur da suke haka da ganga 411,000 a cikin watan Yuli mai zuwa. Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiya ya bayyana cewa kungiyar da kawayenta sun gudanar da taro ta kafar sadarwa ta Bidiyo a ranar 3 ga watan mayu wato jiya inda suka tsaida wannan shawarar.
Labarin ya kara da cewa kungiyar tana son ta maida ganga miliyon 2.2 da suke rage da radin kansu a shekarun bayana a hankali-a hankali. Sannan kungiyar zata ci gaba da gudanr da taro a farkon ko wani wata don sanin yadda kasuwar man take a duniya da kuma yadda zasu ci gaba da kara yawan man da suke haka a ko wani wata har zuwa lokacinda zasu kai mizanin da suka amince da kansa. Don haka taronsu nag aba zai kasance a cikin watan Yuli mai zuwa.