OPEC Da Kawayenta Zasu Kara Yawan Man Da Suke Haka A Karon Farko Tun Shekara Ta 2022

A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC +  za su kara yawan man

A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC +  za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna cewa kungiyar OPEC + bata kara yawan man da take haka ba na lokaci mai tsawo, amma a halin yanzu zata kara kamar yadda aka sanar.

Labarin ya kara da cewa kungiyar tana rage ganga miliyon 5.85 wanda kuma shi ne kashi 5.7%  na yawan man da ake haka a duniya, wannan kuma ya yi dai dai da shawarar da OPEC + suka dauka tun shekara ta 2022.

Labarin ya kara da cewa kasashen kungiyar sun amince da haka daga ciki har da kasar Rasha kasar da ta fi ko wace kasa hakar mai a duniya.

Akwai jitajitan cewa Amurka zata kara takurawa Iran a cikin watanni masu zuwa, amma Iran ta ce hakan ba zai shafi ta ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments