Kungiyar ta kasashen musulmi ta ( OIC) ta fitar da bayani a jiya Juma’a tana mai cewa kai hari da Isra’ila take yi akan cibiyoyin kiwon lafiya da su ka hada da Abisitoci da kama ma’aikatan kiwon lafiya da tsare su, yana cin karo da dokokin kasa da kasa da na ‘yan’adamtaka haka nan kuma kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Kungiyar ta OIC ta yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na tsagaita wutar yaki a Gaza, su kuma dorawa Isra’ila alhakin abinda take yi.
Har ila yau kungiyar ta OIC ta kuma bukaci ganin kungiyoyin kasa da kasa da su kare cibiyoyin kiwon lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya, haka nan kuma hakkin wadanda su ka jikkata da su sami magani.
Kungiyar ta kasashen musulmi ta kuma jaddada wajabcin samarwa da Falasdinawa cibiyoyin kiwon lafiya a fadin zirin Gaza.
A jiya juma’a da marece ne dai Ministan kiwon lafiya na Gaza, Munir al-Burshi ya sanar da kona asibitin Kamal Adawan a cikin garin Beit Lahiya, bayan da su ka kutsa cikinsa da kuma kona dukkanin kayan da suke cikinsa.
A gefe daya kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta karyata zargin da HKI ta yi na cewa da akwai mayakan kungiyar a cikin Asibitin.
Hamas ta cigaba da cewa abinda Isra’ilan take nufi da hakan shi ne bai wa laifin da take tafkawa a cikin asibitin fuska ta halarci.