Kamfanin hakar Uranium na kasar faransa Orano, ya sanar da cewa gwamnatin Nijar ta kwace masa lasisin hakar Uranium a yankin Imouraren dake arewacin kasar Nijar.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar yau Alhamis, ya ce yayi na’am da matakin na Nijar, duk da yunkurinsa na fara aikin.
Kamfanin Orano S.A, ya kuma ce yana da hakkin kalubalantar matakin gaban kotunan da suka dace ko na kasa ko kuma kasa da kasa.
A kwanan nan dai bayanai sun ce kamfanin ya dan soma aikinsa bayan da gwamnatin Nijar ta dibar masa wa’adin zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2024 nan na ya fara aikin ko kuma a kwace masa lasisin.
Wasu ‘yan Nijar da dama na alakanta matakin da sabuwar huldar da kasar ta kulla da Rasha da ma Iran akan batun makamashin.