Najeriya: Tace Man Fetur A Cikin Gida Zai Magance matsalar Karancinsa – NBA

Babbar kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta bukaci a gaggauta aiwatar da umarnin shugaban kasa Bola Tinubu kan batun samar da danyen mai ga matatar

Babbar kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta bukaci a gaggauta aiwatar da umarnin shugaban kasa Bola Tinubu kan batun samar da danyen mai ga matatar man Dangote da sauran matatun mai na cikin gida.

Yakubu Maikyau, Shugaban NBA kuma Babban Lauyan Nijeriya (SAN), ya bayyana haka

Kungiyar kwararrun lauyoyi ta bayyana kafa matatar a matsayin kishin kasa, kuma ta bukaci gwamnatin tarayya da ‘yan Nijeriya da su marawa matatar man Dangote baya domin kawo karshen matsalar karancin man fetur da layukan da aka saba yi a gidajen man kasar nan.

Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda matatar ke fuskantar kalubale mai karfi daga masu shigo da mai, wadanda suka durkusar da tattalin arzikin kasar ta hanyar shigo da albarkatun man fetur da aka tace a kasashen waje, duk kuwa da shaharar Nijeriya a matsayin kasa ta kan gaba a fannin samar da danyen mai a duniya.

Maikyau, wanda ya jagoranci sauran shugabanni da mambobin kungiyar a ziyarar da suka kai matatar, ya yabawa Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, bisa jajircewarsa duk da adawar da yake fuskanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments