Nasarallah: Kissan Kiyashin HKI Ya Farkarda Hankalin Mutanen Kasashen Yamma

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kissan kiyashi da kuma ta’asar da sojojin HKI suke yi a gaza

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa kissan kiyashi da kuma ta’asar da sojojin HKI suke yi a gaza ya farkadda hankalin mutanen kasashen yamma.

Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Nasarrallah yana fadar haka a taron Ashorra rana ta biyu, a dakin taron ‘ Sayyed al-Shuhada’ da ke kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon a jiya Lahadi.

Ranakunan muharram ko Ashoora dai ranakune na makoki ga mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) da kuma dukkan musulmi saboda kissan da aka yiwa Imam Hussain (a) limami na 3 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), jikan manzon All..(s) wanda ya faru a ranar 10 ga watan Muharram na shekara 61  bayana hijira.

Sayyid Hassan Nasarallah  ya kara da cewa kungiyarsa ta tsaida shawarar shiga yakin tufanul Aksa ne saboda taimakawa al-ummar Falasdinu wadanda hKI da magoya bayanta suke wa kissan kiyashi a Gaza.

Ya kuma kara da cewa mafi yawan masana masu hankali wanda suke tare da su, sun bayyana wa kungiyar kan cewa sun dauki matsayin da ya dace a Tarihi tare da shiga yakin Tufanul Aksa.

Ya kuma kammala da cewa kungiyar zata ci gaba da yaki da HKI ko da ya kai ga fito na fito a cikekken yaki a kan kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments