Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi sun cimma yarjejeniya

kasashen afrika ta yamma guda 3 cimma yarjejeniyar tsaro da yaki da ta'addanci dake addabar su

Najeriya ta sanar da wani shirin tsaro tsakaninta da Kamaru, Chadi da Nijar wanda zai bai wa sojoji damar bin ƴan bindiga har zuwa kilomita 5 a cikin iyakokin kasashen juna.

Ministan tsaron Najeriya Christopher Musa ne ya bayyana cimma wannan yarjejeniya, a matsayin wani bangare na kokarin da ake yi na karfafa hadin kai don yakar ta’addanci, da ayyukan ƴan bindiga da kuma manyan laifuka da ake aikatawa a tsakanin kan iyakoki.

A cewar Musa, yarjejeniyar ta bai wa jami’an tsaro takaitaccen ikon bin sawun mayaka da yan bindiga wadanda ke kokarin tsere wajen kai musu farmakin sojoji ta hanyar tsallakawa kasashe makwabta.

Wannan yarjejeniyar za  ta amfani yankin arewa mai nisa na Jamhuriyar Kamaru, inda rashin tsaro da ke da nasaba da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka shafi al’umomin da ke kan iyakar kasar da Najeriya tsawon shekaru. Sai dai har yanzu babu cikakken bayani akan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar, ciki har da sharuɗan aiki da kuma yadda za a kare lafiyar fararen hula.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted