Najeriya: Ana Fargabar Sake Tashin Farashin Fetur Bayan Dangote Ya Daina Sayar Da Mai A Naira

’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur

’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira.

Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka.

An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai.

Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira.

Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa.

Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya dauka ba, hakan ya sa Dangote ba shi da wani zabi illa ya fara siyan danyen mai da dala.

“Yanzu matatun cikin gida sai sun samu dala kafin su iya ci gaba da aiki.”

Matatar Dangote ta ce, “Dole ne mu daidaita kudin sayar da kayayyakinmu da kudin da muke siyan danyen mai. Yarjejeniyar Naira ba ta samar da isasshen danyen mai da zai iya kula da aikinmu ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments