Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5, 

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaron kasashen pakistan da Afghanistan sun yi musayar wuta mai tsananin a iyakokin kasashensu, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 5,  hakan na nuna irin rikicin dake tsakanin kasashen masu makwabtataka da juna, bayan sun cimma yarjejeniyar sulhu a kasar saudiya amma da alama babu ci gaban da aka samu.

A wani sakon da kakakin gwamnatin Taliban ya wallaka a shafinsa na x zabihullah majahid yace sojojin kasar Pakistan sun kaddamar da hari a wani yanki dake lardin kandahar na kasar Afghanistan da hakan yasa sojojin su  mayar da martani.

Sai dai ana sa bangaren firaministan kasar Pakistan Shebaz sharif ya ce sojojin kasar afgahnistan ne suka fara harbe harbe a iyakar chaman,

Dangantaka tsakanin Afghanistan da Pakistan ta kara tabarbarewa ne a yan watannin baya bayan nan, inda rikici ya kara Kamari tsakaninsu a iyakokin kasar duk da tattaunawar sulhu da ka yi a a Qatar da kuma na bayan bayanna a kasar saudiya amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted