Mutane 2,822 Isra’ila Ta Kashe A Lebanon

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa a kalla mutane 2,822 ne suka rasa rayukansu sannan wasu 12,937 suka samu raunuka tun farkon

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa a kalla mutane 2,822 ne suka rasa rayukansu sannan wasu 12,937 suka samu raunuka tun farkon harin da Isra’ila ta kai kan kasar Lebanon.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kai a yankuna daban-daban na kasar Lebanon, mutane 30 ne suka yi shahada, yayin da 165 suka jikkata.

A cikin lokaci guda makiya sun kai hare-hare ta sama 101 a yankuna daban-daban na kasar Lebanon.

A cewar wani rahoto da kwamitin gaggawa na kasar Labanon ya fitar, an kashe jami’an kiwon lafiya 172 tare da jikkata wasu 233 sakamakon harin da Isra’ila ta kai.

Asibitoci 39, da cibiyoyin kiwon lafiya da na gaggawa 80, da motoci 242 sun lalace a hare-haren da Isra’ila ta kai.

A safiyar yau alhamis, wani hari da Isra’ila ta kai a garin Deir al-Zahrani da ke gundumar Nabatieh, ya kashe akalla mutane uku.

Masu aikin ceto na neman wadanda suka tsira a karkashin baraguzan ginin.

A ranar Larabar da ta gabata, Isra’ila ta tsananta kai hare-hare ta sama a wasu gundumomi biyu na birnin Baalbek mai dimbin tarihi, inda suka kashe a kalla mutane 19, ciki har da mata takwas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments