Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare masu muni a yankunan tsakiyar Gaza da Khan Yunus, wanda hakan ya yi sanadiyyar kara samun hasarar rayuka tsakanin Falastinawa fararen hula masu yawa, da kuma haifar da wata sabuwar gudun hijira a yankin Khan Yunus.
Yakin kisan kare dangi na Isra’ila a kan al’ummar Gaza ya shiga rana ta 321, yayin da take ci gaba da kai wasu hare-haren a dukkanin yankunan Zirin ta sama da kasa da ta ruwa.
Sakamakon hare-hare na baya-bayan nan da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan fararen hula da iyalan Falasdinawa a zirin Gaza, fararen hula hudu daga dangi daya sun yi shahada a arewacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, kuma wasu da dama da suka jikkata, an kuma kai wasu daga cikinsu asibitin Al Awda da ke arewacin sansanin.
A cikin birnin Gaza, unguwar Al-Zaytoun ta fuskanci hare-haren wuce gona da iri tare da ruwan bama-bamai da jiragen yaki, an kuma kai wani harin da bindigogin atilari na sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila a kan gidajen mutane dake kan titin Kashko a unguwar Al-Zaytoun.