Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Iran ba za ta nemi taimakon kowa ba don kare kanta
Kakakin gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta tabbatar da cewa: Iran ba za ta nemi izini daga kowane iko don kare kanta ba, kuma sojojin kasar ne ke da alhakin kare ƙasarsu. Ta jaddada cewa duk wani hari zai haifar da sakamako, tana mai cewa, “A sani cewa duk wani mataki na kai hari da makiya zasu kaddamar ba zai kasance babu kashe kuɗi ko mummunan sakamako da zasu haifar wa kansu ba.”
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran, mai magana da yawun gwamnatin Iran ta rubuta a cikin sanarwarta a ranar Asabar cewa: “A cikin kwanakin nan, maƙiyan Iran suna magana game da makomar wata ƙasa, suna da’awar ikon lalata ta, kamar dai shawara ɗaya za ta iya share wata ƙasa daga taswirar duniya da kawo karshen wayewarta daga shafin tarihi.”
Ta ƙara da cewa, “Wannan ikirarin yana bayyana girman kai, yaudarar kai da kuma rashin hankali gami da jahiltar wacce ce Iran – ƙasa wadda tushenta ya zurfafa a cikin dubban shekaru na tarihi – da kuma rayuwar mutanenta daban-daban. Waɗanda suke irin wannan barazanar ba su taɓa sanin Iran ko nufin mutanenta ba, kuma ba su da ikon cimma irin wannan ruɗanin tunaninsu.”
Kakakin gwamnatin ta ci gaba da cewa: “Jami’an Amurka da masu mulkin haramtaccyar kasar Isra’ila su sani cewa: Makomar Iran ba ta dogara a kan manufarsu ba, kuma wannan al’umma ba za ta mika ‘yancinta da hakkokinta ga masu mata barazana ba”.