Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani, ya tattauna da tokwaransa na kasar Jordan Ayman Al-Safadi inda suka tabo batutuwa da dama daga ciki har da batun yakin gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Al-Safadi ya isa birnin Tehran a jiya Lahadi kuma ana saran zai hadu da wasu manya manyan jami’an gwamnati a nan Tehran inda zasu tattauna al-amura da suka shafi kasashen yankin da kuma kasa da kasa. Har’ila yau da kuma hulda tsakanin kasashen biyu.
Al-Safadi ya bayyana cewa zai isar da sakon sarkin Jordan, Sarki Abdullahi II ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan. Ya kuma kara da cewa baya dauke da sako daga HKI, sakon nasa na kyautata dangantaka da kasar Iran ne kawai.
Kafin haka dai ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani, a shafinsa na X ya ce ya zanta ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen kasashen Masar da kuma Jordan kafin na kawo ziyara zuwa Tehran.