Rahotanni da suka fito daga Najeriya sun nuna cewa ministan tsaro Alh mohammadu Badaru Abubakar a ranar 1 ga watan Decemba ya mika takardar ajiye aiki a matsayinsa na ministan tsaron kasa, saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa,
Kamar yadda kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba tinubu ya amince da takardar neman ajiye aikin, kuma ya gudemasa game da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasarsa, tuni kuma aka fara lalubo wanda zai maye gurbinsa domin mika sunansa ga majalisa don a tantance shi.
Badaru Abubakar dan shekara 63 da haihuwa shi ne gwamnan jihar jigawa har na tsawon zango biyu wato daga shekara ta 2015 zuwa ta 2023 kuma shugaban kasa tunubu ya nada shi a mukamin minister a ranar 21 ga watan Agusta shekara ta 2023
Ya ajiye aikin ne adai dai lokacin da shugaba tunubu ya sanya dokar ta baci kan tsaro a fadin kasar,da zimma kawo karshen matsalar tsaro da kasar take fama da shi .