Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude.
Jaridar Middle eart Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Al-shaibani ya na cewa takunkuman suna hana ruwa guda a cikin al-amura da dama a kasarsa, kuma suna hana kafuwar gwamnatinsa su kamar yadda ya dace.
Ministan ya ce dage takunkuman ya zama wajibi don samun ci gaban kasar don kuma rage matsin lamban da mutanen kasar suke ciki. Kasashen yamma musamman Amurka da tarayyar Turai da kuma MDD sun dorawa gwamnatin tsohon shugaban kasar Bashar al-asada takunkuman tattalin arziki, don bawa yan tawayen da suke taimakawa nasara a yakin basabsan da aka dauki shekaru kimani 14 ana fafatawa a kasar.
Ya zuwa yanzun dai kasashen Burtaniya da tarayyar Turai da kuma Amurka duk sun daukewa kasar wasu takunkuman tattalin arzikin. Amma har yanzun akwai wasu da dama wadanda ba’a dauke ba.