Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Mayar Da Martani Kan Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani ga kungiyar hadin kan kasashen Larabawa tana mai jaddada matsayinta na bukatar ganin an samun kwanciyar hankali

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani ga kungiyar hadin kan kasashen Larabawa tana mai jaddada matsayinta na bukatar ganin an samun kwanciyar hankali a Siriya da kuma hana hargitsi

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi wanda ya ziyarci birnin Beijing na kasar China domin tuntubar jami’an kasar, ya mayar da martani ta hanyar rubuta a shafinsa na twitter ga zargin kasashen Larabawa, inda ya bayyana matsayin Iran kan sabuwar kasar Siriya tare da ba da shawarwari ga shugabannin kasashen Larabawa.

Araqchi ya bayyana cewa: “Ya ku ‘yan uwa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, Iran ma kamar ku ce, tana son ganin an samun kwanciyar hankali, zaman lafiya da kuma dakile hargitsi a Siriya, saboda dalilai na fili:

Kiyaye mutunci da amincin kasar Siriya da hadin kan yankin Gabas ta Tsakiya, tabbatar da tsaron dukkanin kabilu da addinai, ciki har da ‘yan Sunna, Shi’a, Alawiyawa da Kurdawa, kula da aminci da hurumin wuraren addini, dakile watsuwar makamai a hannun jama’a, rashin tsoma bakin kasashen waje a harkokin da suka shafi cikin gidan kasar ta Siriya, hana kasar Siriya zama matattaran ‘yan ta’adda da masu tsaurin ra’ayin addini da masu wuce gona da iri don kada kasar ta kasance hatsari ga makwabtanta dama yankin gaba daya.

Araqchi ya jaddada cewa: Akwai buƙatar amfani da hankali da hadin kai da nisantar rarrabuwa da kare muradun mazhaba ido rufe. Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana tare da sauran kasashen yankin kan bukatar mika ragamar shugabancin Siriya ga sabbin jami’anta cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kafa gwamnati da zata hada dukkanin bangarori da kabilu da addinai na kasar, kuma Iran a shirye take ta taimaka wajen cimma manufofin da ta ambata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments