Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Saudiyya, Lebanon Da Uzbekistan

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwaransa na Saudiyya a birnin New York na Amurka Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da

Ministan harkokin wajen Iran ya gana da takwaransa na Saudiyya a birnin New York na Amurka

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na Saudiyya Faisal bin Farhan, a jiya Lahadi, a birnin New York na Amurka, a gefen zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na Amurka.

Ministocin biyu sun mika goron gayyata a tsakaninsu kowa yanagayyatar takwararsa ga ziyarar kasarsa.

Har ila ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da takwaransa na kasashen Lebanon da Uzbekistan a gefen zaman taron babban zauren na Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York, inda ya tattauna da su kan batutuwan da suka shafi bangarorin kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments