Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babu wata doka ko tsari da Iran za ta bi wajen kare al’ummarta
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta kiyaye wata doka ko tsari ba wajen kare al’ummarta daga duk wani matakin wuce gona da iri.
Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a lokacin da ya isa birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki cewa, manufar ziyararsa zuwa Iraki ita ce tattaunawa da juna da karfafa hadin kai da kasar Iraki dangane da batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.
Ministan harkokin wajen Iran ya kara da cewa: Suna hada kai ne don dakile aniyar yahudawan sahayoniyya da kuma kokarin da suke yi na kokarin fadada tashin hankali a yankin.
Araqchi ya jaddada cewa: Babu wanda ke son fadada yakin sai ‘yan sahayoniyya, ya kuma kara da cewa: Burin kowa da kowa shi ne hana bullar wata sabuwar bala’i da za ta iya janyo fadadar masifa a yankin.