Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci ya kai ziyara zuwa kasar Masar a cikin tawagar shugaban kasa domin halartar taron kungiyar D-8, ya rubuta a shafinsa na X cewa: Iran da Masar suna da al’adu da kamanceceniya iri daya da tushensu shi ne tarihi, wadanda kuma bayan bayyanar manzon rahama annabi Muhammad ( s.a.w) sun wadannan al’adun sun kara karfafa.
Arakci ya rubuta cewa: Na sami dacen ziyartar wuraren na musulunci da tarihi a cikin birnin alkahira da su ka hada da Masallacin Imam Husaini ( a.s) da masallacin Sayyidan Zainab (a.s) da Masallain Sayyidah nafiah, da kuma masallacin Muhammadu Ali Pasha.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce: A masallacin Muhammad Ali Pasha wanni mai fasahar zane a jikin dutse dan asalin kasar Iran ya rubuta wasu baitocin waka a makabartar Muhammad Ali Pasha a shekarar hijira ta 1262.:
Har ila yau Arakci ya yi ishara da shahararren marubucin nan dan kasar Masar, Najib Mahfuz wanda ya sami kyautar Nobel ta adabi. Ya kuma nakalto wasu baitocin wakarsa da a ciki ya siffata kyawun birnin Shiraz na Iran da mawakin na Masar ya taba ziyarta.