Araqchi: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi  Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Haɗin kai tsakanin kafofin watsa labarai, diflomasiyya da fage na tabbatar da ƙarfi da ci gaban ƙasa A

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Haɗin kai tsakanin kafofin watsa labarai, diflomasiyya da fage na tabbatar da ƙarfi da ci gaban ƙasa

A jajibirin ranar ‘yan jarida ta kasa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ziyarci hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBO) inda ya gana da shugaban kungiyar da sauran jami’an kafofin yada labarai na kasar.

A yayin taron, shugaban kungiyar ta NBO, Peyman Jebli, ya yi maraba da minista Araqchi, ya kuma yaba da kokarin da hukumomin diflomasiyya ke yi wajen inganta manufofin harkokin waje da kuma kare muradun kasar.

Mista Jebli ya bayyana hadin kai da hadin gwiwa tsakanin harkokin diflomasiyya da kafafen yada labarai da cewa yana da matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro da ikon kasa, sannan ya jaddada cewa NBO na samun ci gaba a wannan fanni.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar ya godewa shugabanni da daraktoci na sassa daban-daban na NBO bisa muhimmiyar rawar da NBO ke takawa wajen tallafawa ayyukan hukumar diflomasiyya. Ya yi la’akari da hadin kai da hadin gwiwa a tsakanin kafofin yada labarai da diflomasiyya don samun nasarar kasar wajen tabbatar da moriyar kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted