Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara.
Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu..
Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma da abinda ya shafi noma a duniya. Taron na Brazil zai maida hankali kan aminci samun abinci ga yan kasashen kungiyar da kasuwancinsa a duniya. Da kuma hanyoyin samar da samar da kudade don ayyukan noma duniya.
Daga karshe taron na Brazil zai bayyana jadawalin ayyukan kungiyar dangane da noma a shekara ta 2025.