Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira
Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa.
Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma sha biyar masu zuwa. Ya ci gaba da cewa: Za su mayar da dukkan mazauna Gaza zuwa garin Jabaliya bayan an dawo yaki, kuma Falasdinawa ba za su ga wani abin neman ba har abada.