Jiniyar gargadi ta kada a cikin sassa masu yawa na Falasdinu dake karkashin mamaya bayan harbo makami mai linzami da mutanen Yemen su ka yi.
Kafafen watsa labarun HKI sun ce, jiniyar gargadin ta kada a cikin garuruwa 255 a HKI daga cikin har da birnin Kudus.
Jaridar “Yediot Ahronot” ta buga labarin dake cewa, wasu barguzan makami mai linzamin sun fada a unguwar “Mifo Hurun” dake Tel Aviv.
Har ila yau harba makami mai linzamin daga Yemen ya sa an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin saukar jiragen sama na “Ben Gorion”.
Jaridar “Yesrael Home” ta ce miliyoyin mutane ne su ka shiga dakunan boya saboda kaucewa makami mai linzamin da aka harbo daga Yemen.
A jiya Laraba Sayyid Abdulmalik al-Husi, jagoran kungiyar Ansarullah ya yi alkawalin ci gaba da kai wa HKI hare-hare har zuwa lokacin da za a kawo karshen kai wa Gaza hari, da kuma dauke takunkumin hana shigar da kayan agaji zuwa yankin.
Sayyid Abdulmalik Husi ya kuma kara da cewa, al’ummar Yemen za su ci gaba da yin duk abinda ya dace a kowane mataki domin taimaka wa al’ummar Falasdinu, ta hanyar kai wa HKI hari.
Tun a cikin watan Nuwamba na 2023 ne dai al’ummar Yemen su ka fara kai wa HKI hari a matsayin taya Falasdinawa fada, haka nan kuma sun hana duk wani jirgin ruwa mai zuwa HKI wucewa ta tekun “Red Sea”.
A gefe daya, Amurka da Birtaniya suna ci gaba da kai wa Yemen hare-hare a karkashin kare HKI da suke yi.