MDD: Sauya Wa Falastinawa Wurin Zama Ya Sabawa Doka Da Ka’ida

A cikin wani bayani da mai Magana da yawun bababn sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, daukar duk wani mataki na tilasta Falastinawa mazauna

A cikin wani bayani da mai Magana da yawun bababn sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, daukar duk wani mataki na tilasta Falastinawa mazauna zirin Gaza kauracewa muhallansu ya yi hannun riga da dukkanin ka’idoji da dokoki na kasa da kasa.

Wanann yana zuwa ne a daidai koacin da rundunar Sojin Isra’ila take bayar da wata sabuwar sanarwar tilasta falastinawa yin kaura, inda ta umarci mazauna wasu unguwanni a tsakiyar Gaza su yi hijira.

Mai magana da yawun sojin Avichay Adraee ne ya sanar da hakan inda ya ce mazauna rukunin gidaje na 2232 zuwa 2240 da ke unguwar Maghazi da kuma waɗanda ke unguwannin Salah El-Din, El-Farouk da kuma El-Amal duk a tsakiyar Gaza su yi hijira daga wuraren.

Sojojin sun yi ikirarin cewa wuraren na cikin mummunan hatsari sakamakon yaƙin da ake yi da Hamas.

Isra’ila ta kashe akalla mutane shida ta kuma jikkata mutum uku a wani hari da ta kai rukunin gidajen zama a birnin Nabatieh, a kudancin Labanan, a cewar Ma’aikatar Lafiyar Labanan.

Ana ganin tashe-tashe hankula matuka a yankin a cikin ’yan makonnin nan, musammana  lokacin da yahuda suke cikin firgici na jiran martanin Iran da Hizbullah, wanda haka yasa Isra’ila take ta kokarin dauke hankulan al’ummomin duniya daga irin babbar matsalar ad take ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments