Mayakan Hizbullah Sun Kai Farmaki Da Makamai Masu Linzami Fiye Da 100 A Kan Birnin Haifa Da Wasu Wurare A HKI A Safiyar Yau Talata

Dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun kai farmaki kan birnin Haifa da wasu garuruwa a kasar Falasdinu da aka mamaye sa safiyar yau Talata.

Dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun kai farmaki kan birnin Haifa da wasu garuruwa a kasar Falasdinu da aka mamaye sa safiyar yau Talata.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto majiyar kungiyar tana fadar haka, sannan kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da labarin. Tashar talabijin ta HKI ‘Channel 12’ makaman Hizbulla 5 ne suka fada kan wani gini a tekun Haifa. Sannan majiyar sojojin yahudawan ta tabbatar da cewa kungiyar Hizbullah ta cilla makamai 105 kan garuruwan Haifa da Kiryat Yam. Banda haka an kai mutane da dama asbiti saboda raunukan da suka ji. Amma kamar yadda suka saba suna boye yawan wadanda suka rasa rayukansu.

Majiyar ta kara da cewa wannan shi ne hari mafi muni wanda kungiyar ta kai kan garin Haifa tun lokacinda aka fara yakin Tufanul Aksa fiye da shekara guda da ta gabata. A hare haren HKI mafi muni a kan kasar Lebanon inda a lokaci suka jiragen yakin HKI suka jefa ton  80 na makamai a kan wasu gine gine, inda suke zaton yana cikin daya daga cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments