Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran a cikin al-amuran sharia da kuma na harkokin kasashen waje, yana tir da da allawadai da mataimakiyar shugaban hukumar ICJ mai hukunta manya-manyan laifuka ta duniya, Julia Sebutinde wacce ta bayyana a fili tana goyon bayan HKI a yakinn Gaza.
Labarin ya kara da cewa, mataimakin ministan Kazem Gharibabadi ya bayyana kidemewarsa da abibda alkalar ta fada, ya kuma bayyana cewa hakan wani ci baya ne a cikin aikin alkalanci a wannan babban kotun,
A ranar 10 ga watan Augustan da muke ciki ne Sebutinde ta bayyana a fili kan cewa Ubangijinta ya umurceta da ta tsaya a bangaren HKI , Sanna alamun tashin kiyama sun bayyana a gabas ta tsakiya.
A shekarar da ta gabata ma mai shariar sebutinde ta tsaya a gaban alkalain kotun 17 wadanda suka tabbatar da cewa HKI ta aikata laifukan yaki a gaza. Ta ce ba haka bane. Mataimakiyar alkalin kutun yar kasar Uganda sebutinde ta sabawa gwamnatin kasarta, sannan gwamnatin kasar Uganta tace ta barranta daga matsayinta.