Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu.
Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu.
A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada bukatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma bukaci Tarayyar Turai su hada kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro.
Shugaba Tinubu ya tabbatar da kudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar hankali.
A taron G20 da aka yi a Afirka Ta Kudu, Tinubu ya bukaci shugabannin duniya su samar da tsarin kudi na kasa da kasa, tare da magance matsalolin bashi.
Ya ce tsarin da ake amfani da shi a yanzu ya zama tsohon yayi, kuma bai dace da kalubalen wannan zamani ba. ya kuma nemi a samar da ka’idojin duniya da za su tabbatar da cewa kasashen da ke samar da muhimman ma’adanai ciki har da Nijeriya, suna amfana da su.