Masu Gwagwarmaya A Iraki Sun Kai Sabbin Hare Hare Kan Wasu Wurare A HKI

Dakaru masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar Iraki sun kai sabbin hare hare kan wasu wurare masu muhimmanci a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Dakaru masu gwagwarmaya da yan ta’adda a kasar Iraki sun kai sabbin hare hare kan wasu wurare masu muhimmanci a kasar Falasdinu da aka mamaye.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mayakan Hashdushabi na fadar haka a shafinsu na Telegram. Sun kuma kara da cewa sun yi amfani da makaman ‘Drones’ ko jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, masu kunan bakin wake, kan wurare masu muhimmanci a kusa da kogin Jordan da kuma birnin Haifa cibiyar tattalin arzikin HKI.

Labarin ya kara da cewa dakarun sun kai wadan nan hare haren ne don tallafawa Falasdinawa wadanda HKI take wa kisan kiyashi fiye da shekara guda a Gaza, da tallafawa mutanen kasar Lebanon wadanda HKI take kashewa a kudancin kasar.

Dakarun Hashdushaabi sun kara jaddada cewa zasu ci gaba da kai wadan nan hare hare kan HKI har zuwa lokacinda HKI za ta kawo karshen kissan Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments