Masar ta sanar da kashe daya daga cikin mayakanta a musayar wuta da sojojin Isra’ila

Rundunar sojin Masar ta fitar da sanarwa dangane da harbe-harben da aka yi tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila a Rafah. Kakakin rundunar sojin Masar

Rundunar sojin Masar ta fitar da sanarwa dangane da harbe-harben da aka yi tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila a Rafah.

Kakakin rundunar sojin Masar ya bayyana cewa: Dakarun sojin Masar na gudanar da bincike daga hukumomin da suka dace dangane da harin da aka kai a yankin Rafah da ke kan iyaka, wanda ya yi sanadin shahadar daya daga cikin jami’an tsaron.

Kakakin rundunar sojin Isra’ila Afikhai Adrei ya sanar da cewa: A ‘yan sa’o’i kadan da suka gabata an yi harbe-harbe a kan iyakar Masar, kuma muna gudanar da bincike kan lamarin, muna kuma tattaunawa da bangaren Masar kan wannan batu.

Shafin “Walla”, na gwamnatin Isra’ila ya ce an kashe ‘yan kasar Masar biyu a wata musayar wuta da sojojin Isra’ila suka yi da su a mashigar Rafah, amma bangaren Masar din bai ce komai ba bayan haka.

Ita ma jaridar “Maarif” ta Isra’ila ta bayyana “kashe wani sojan Masar a lokacin arangamar da aka yi tsakanin sojojin Masar da na Isra’ila a mashigar Rafah”.

Jaridar ta yahudawa ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila sun yi musayar wuta da sojojin Masar bayan da sojojin Masar suka bude wuta kan dakarun Isra’ila a cewar sojojin Isra’ila, kuma ana gudanar tuntuba tsakanin bangarorin biyu kan batun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments