Masar: Aikin Sojen Kasar Zai Takaita Wajen Kare Saudia Ne Lawai

Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assini ya bayyana cewa aikin sojen da zasu yi a kasar Saudiya, zai takaita ne kawai wajenkare kasar daga makaman Yemen,

Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assini ya bayyana cewa aikin sojen da zasu yi a kasar Saudiya, zai takaita ne kawai wajenkare kasar daga makaman Yemen, amma ba zasu cilla makamai kan kasar Yemen ba.

Tashar talabijan ta al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa, sojojin masar ba zasu shiga wata kasa ba, sannan ko a saudia ba zata cilla makamai zuwa cikin kasar Yemen ba. Sojojin kasar zasu takaita ayyukansu newajen kara kasar da saudia daga makaman kasar Yemen.

A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Assisi ya bukaci majalisar dokokin kasar tabashi izinin tura sojoji zuwa kasar Saudia don kareta daga makaman kasar Yemen.

A wani labarin kuma Shiekhil Azhar Ahmad Attayyib ya bukaci a kafa tawagar amintattu masu shiga tsakani daga cikin kasashen larabawa don kokarin sasanta matsalolin yake yaken da suke faruwa a cikin kasashen larabawa.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted