Mali Ta Katse Huldar Diflomasiyya Da Ukraine

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali, ta sanar da katse huldar diflomasiyya dake tsakaninta da kasar Ukraine nan take. Gwamnatin ta sanar da haka ne

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali, ta sanar da katse huldar diflomasiyya dake tsakaninta da kasar Ukraine nan take.

Gwamnatin ta sanar da haka ne jiya Lahadi, inda ta ce ta lura da wani furuci da ya raina ikon mulkinta da kakakin hukumar leken asiri ta sojojin kasar Ukraine Andrii Yusov ya yi a baya bayan nan, wanda ke tabbatar da hannun Ukraine cikin wani harin wasu kungiyoyi ‘yan ta’adda, da ya rutsa da mutane tare da lalata dukiyoyi ga sojojin Mali, a yakin da suke a arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta bayyana matakin hukumomin Ukraine a matsayin wanda ya take ‘yancin kan Mali, ya kuma zarce lamarin da kasa da kasa za su iya shiga tsakani, haka kuma takala ce a bayyane ga kasar.

Don haka, gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali ta yanke shawarar katse huldar diplomasiyya nan take da kasar ta Ukraine, in ji kakakin gwamnatin kasar Kanar Abdoulaye Maiga.

A Ranar Litinin din da ta gabata rundunar sojin Mali ta tabbatar da mutuwar sojoji da dama sakamakon ba-ta-kashi da dakarun kasar suka yi da ‘yan ta’adda a yankin Tinzaouaten da ke arewacin kasar.

Kazalika rundnar sojojin haya ta Rasha mai suna Wagner da ke goyon bayan sojojin Mali ta tabbatar da mutuwar mayakanta ciki har da wani kwamanda a ba-ta-kashin.

Zarge-zargen, da babu wanda ya musanta, sun nuna cewa jami’an gwamnatin Ukraine suna goyon bayan ta’addanci a Afirka, da yankin Sahel musamman ma a Mali,” in ji shi.

Don haka gwamnatin Mali za ta mika lamarin gaban hukumomin shari’a da suka dace.

Kanar Maiga, ya ce za su gabatar da batun ga hukumomin Afirka da na kasashen duniya tare da hujjojin da ke nuna cewa Ukraine tana goyon bayan ta’addanci a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments