Kakakin rundunar sojin kasar iran ya bayyana cewa duk wa ni karfi da ya kuskura ya fuskancin karfin kasar iran da ya samu kwarin guiwa daga taimakon ubangiji to babu abin da zai girba banda faduwa da rugujuwa da kuma shan kunya a idon duniya
Brigediya janaral abulfazal shekarci yayi bayyani game da ci gaban da aka samu ciki har da koma bayan da shugaban Amurka Donald trump ya samu da kuma mummunan kayen da ya sha a zaben yan majalisa na tsakiyar waadi da aka gudanar a kasar tare da jam’iyarsa ta republican dama sauran magoya bayansa,
Yace kayen da ya sha ba wai kawai sakamakon sauye –suyen na wucin gadi na siyasa da aka samu acikin gidan Amurka ba ne, yace maimakon haka abin da ya faru yana nuni ne ga gaskiyar alama’ri mai girma da ba za’a iya musantawa ba wato shan kaye a gaban kudurin kasar iran mai karfi
Daga Karshe yace wannan shan kaye a bangaren dabaru da amurke take takama da shi shida ce mai gamsarwa dake nuna cewa ba zaa taba tsara ma’aunin karfi a duniya ta yadda zai amfani kasashen dake neman mallakar duniya baki daya ba.