Makiya Iran, Na Kokarin Wuce Gona Da Iri A Salon Su Na Yakin Rikita Tunani_ Jagora

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce makiya kasar suna kokarin wuce gona da iri a matsayin wata babbar dabara a

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce makiya kasar suna kokarin wuce gona da iri a matsayin wata babbar dabara a yakin da suke yi na Rikita Tunani.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da masu shirya taron shahidan Kohgiluyeh da na lardin Boyer-Ahmad a birnin Tehran a yau Laraba.

Jagoran ya ce a ko da yaushe makiya Iran suna kokarin sanya tsoro a cikin al’ummar kasar.

“Tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, suna kokarin cusa ra’ayin cewa ya kamata mu ji tsoron Amurka, Birtaniya, da sahyoniyawa.”

“Idan har gwamnatocin da a yau suke mika wuya ga bukatun ma’abota girman kan duniya sun dogara ga al’ummominsu da karfinsu to za su iya wargaza anniyarsu.”

Jagoran ya ce Imam Khumaini wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya taimaka wajen kawar da tsoro daga zukatan al’umma tare da sanya kwarin gwiwa da dogoro da kai a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments