Majalisar Zartawa Ta HKI Ta Amince Da Tsagaita Wuta Da Hizbullah A Jiya Talata

Firay ministan HKI Benyamin Natanyahu ya sami amincewar majalisar ministocinsa dangane da abinda ya kira tsagaita bude wuta na wucin gadi tare da kungiyar Hizbullah

Firay ministan HKI Benyamin Natanyahu ya sami amincewar majalisar ministocinsa dangane da abinda ya kira tsagaita bude wuta na wucin gadi tare da kungiyar Hizbullah da kuma gwamnatin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce: Ministoci 10 ne suka amince da tsagaita wutar sannan guda kuma ya ki amincewa.

Labarin ya kara da cewa majalisar zartarwar ta HKI ta amince da hakan ne a tsakiyar daren jiya Talata, inda daga nan shugaban Biden na Amurka ya fito ya bayyana yadda yarjeniyar ta kasance filla filla.

A jawabin da ya gabatar bayan amincewa da yarjeniyar Natanyahu ya fadawa yahudawan Sahyoniyya kan cewa tsawon tsagaita wutar zai kasance kan abinda zai faru a kasar Lebanon nan gaba, amma shi yana ganin ba zai kasance na lokaci mai tsawo ba kuma na din din ba.

Natanyahu ya bayyana abubuwa uku da suka sa ya amince da yarjiyar, kuma sune kauda barazanar Iran, samun damar gabatar da sauye sauye da kara karfin sojojin HKI, da kuma raba Hizbullah da Hamas a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments