Majalisar kare kundin tsarin mulki ta Iran ta kammala tantance sunayen mutanen da suka cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a Iran
Kakakin majalisar kare kundin tsarin mulki ta Iran Hadi Tahan Nazif ya sanar da kammala tantance sunayen mutanen da suka cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shugaban kasa mai zuwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tahan Nazif ya kara da cewa: Bayan kammala tantance cancantar ‘yan takarar shugaban kasa a zaben shugaban kasa karo na goma sha hudu a majalisar kare kundin tsarin mulkin, an aike da jerin sunayen wadanda suka cancanta zuwa ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar.
Abin lura ana shi ne cewa bayan shahadar shugaban kasar Iran Ayatullah Sayyid Ibrahim Ra’isi, za a gudanar da zaben shugaban kasa da wuri na wa’adi na goma sha hudu a ranar Juma’a 28 ga watan Yulin shekara ta 2024 da muke ciki. Sannan mutane 80 ne suka mika takardar neman tsayawa takarar shugaban kasa karo na goma sha hudu a cikin wa’adin da aka kayyade.