Majalisar Dokokin Amurka Ta Kafa Wata Doka Ta Kare Mamayar Da HKI Takewa Kasar Falasdinu

Majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da wata doka wacce zata halatta mamayar da HKI take wa kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv a nan

Majalisar wakilan kasar Amurka ta amince da wata doka wacce zata halatta mamayar da HKI take wa kasar Falasdinu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan dokar tana nufin maida dukkan kayakin da kamfanonin HKI wadanda suke samar da kayayyali  a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, kamar wanda aka samardasu a cikin HKI ne.

Da haka kuma majalisar tana son batar da wadanda suka kauracewa sayan  kayakin da aka kera a HKI.

Labarin ya kara da cewa, yar majalisar wakilai Claudia Tenny ce ta gabatar da bukatar kafa dokar kuma dokar ta sami amincewar majalisar wakilan kasar da rinjaye ba mai yawa sosai ba. Wato 231 da 189. Ana saran dokar zata wuce idan ta je majalisar dattawan makasar.

Manufar kafa wannan dokar dai itace kalubalantar Amurkawa wadanda suke goyon bayan Falasdinawa, kuma suke kira ga sauran yan kasar su kauracewa sayan kayakin da aka samar da su a HKI.

Akwai yahudawan Sahyoniyya kimani 600,000 wadanda suke zaune a yankunan yamma da kogin Jordan tun bayan yakin shekara 1967, yankuna wadanda a bisa kudurorin MDD na Falasdinawa ne.

Kungiyoyi daban daban a kasashen duniya suna yin kira ga kauracewa sayan kayakin da aka kerasu ko aka yi su a HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments