Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce: Falasdinawa Miliyan 2.2 Ne Suke Fama Da Matsalar Karancin Abinci A Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Mutane miliyan 2.2 ne suke bukatar agajin abinci cikin gaggawa a Gaza Hukumar samar da abinci ta Majalisar

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Mutane miliyan 2.2 ne suke bukatar agajin abinci cikin gaggawa a Gaza

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Mutane miliyan biyu da dubu 200 a Zirin Gaza suna ci gaba da bukatar agajin gaggawa bayan shafe tsawon watanni 11 ana gwabza fada a yankinsu, tana mai jaddada cewa rashin aiwatar da umarnin ficewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila daga yankin na Gaza yana ci gaba da kawo cikas ga kokarin da take yi na samar da agaji ga al’ummar yankin.

Hukumar samar da abincin a shafinta a dandalin “X” ta wallafa cewa: Tsawon watannin 11 na yaki a Gaza, har yanzu mutane miliyan 2.2 na cikin tsananin bukatar agajin abinci domin ci gaba da rayuwa.

Ta jaddada cewa: Duk da kudurin da hukumar samar da abinci ta duniya ta yi na bayar da agaji, umarnin korar mutane daga yankin na kawo cikas ga kokarin samar da abinci da al’ummar yankin suke bukata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments