Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Mayar Da Martani Ga Barazanar Trump Kan Cibiyoyin Nukiliyar Iran

Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran Ali

Mai ba da shawara ga jagoran juyin juya halin Musulunci ya mayar da martani ga barazanar shugaban kasar Amurka kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran

Ali Shamkhani mashawarcin Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen siyasa ya jaddada cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta mai tsayayyen tsarin tsaro, al’umma masu tsayin daka, da jajayen layi. Ya jaddada cewa, “tattaunawa hanya ce ta ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba kayan aiki na tilastawa ko mika wuya ba.”

Shamkhani ya rubuta a shafinsa na dandalin X cewa: “Burin isa ga cibiyoyin nukiliyar Iran da kuma ‘tarwatsa su’ ba komai ba ne illa mafarki da shugabannin Amurka da suka gabata sun kasance sun yi has ashen hakan.

Ya kara da cewa: Iran kasa ce mai cin gashin kanta, mai tsarin tsaro mai karfi, mutane masu juriya da jajayen layi. Ya kuma jaddada cewa tattaunawa ita ce hanyar samun ci gaba da kuma kiyaye moriyar kasa da mutunci, ba tilastawa ko mika wuya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted